Yayin da ake bikin cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, lokaci ne da za a waiwayi baya cikin alfahari da nuna sha'awar irin gagarumin tafiya da wannan kasa mai girma ta yi. A cikin shekaru 75 kacal, kasar Sin ta rikide daga kasar da ke fama da yaki, da talauci, ta zama wata kasa mai karfin fada-a-ji a duniya, inda ta samu nasarori da suka bai wa duniya mamaki.